El Rufai Ya Sake Bankado Babban Lamari, Ya Zargi Gwamna Uba Sani da ‘Satar’ Kuɗin Kaduna
Kaduna – Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, ya zargi magajinsa, Sanata Uba Sani, da karkatar da kudaden kananan hukumomi. El-Rufai ya zargi Gwamna Uba Sani da amfani da kuɗaɗen ƙananan hukumomi wajen sayen kadarori a ƙasashen Seychelles, Afirka ta Kudu, da Birtaniya. >>>